Daga Aisha Aliyu Umar
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya taya al’ummar musulmi na Kasar nan murnar zagoyowar watan da aka haifi fiyayyen halitta Annabi S A W.
“A madadin iyalina da tawagata, Ina taya ku murnar wannan lokaci na Maulidi domin tunawa da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad SAW” .
Kadaura24 ta rawaito Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne cikin sakonsa na taya al’ummar musulmi murnar zagoyowar ranar da aka haifi fiyayyen halitta Annabi S A W.
“A lokacin da muke murna da biki a wannan rana, Ina kira ga dukkan ƴan Najeriya dake gida da waje, da su ɗabbaƙa muhimmancin wannan rana. Rayuwar Manzon Allah SAW na koyar da zaman lafiya, ƙauna da haƙuri, waɗanda halaye ne da ya zama wajibi mu yi aiki da su don zama tare a ƙasa irin tamu”. Inji Atiku Abubakar
sanarwa ta Kara da cewa “Kuma a lokacin da muke gaf da yin aiki na tarihi da zai bayyana makomar ƙasarmu, Ina kira gare ku kan ku haɗa hannu waje guda a aikin kuɓutarwa, haɗe kai, sauya fasali da gina Najeriya irin wadda muke mafarkin gani, ƙasar da kowa zai zauna lafiya ba tare da kallon addini, aƙida, yare ko siyasar da yake yi ba”.