Daga Abubakar Lawan Bichi
Mai Martaba Sarki Alh Nasir Ado Bayero ya nada Alh Da’u Sale Tangaji a matsayin Sabon Dagaci garin Tangaji da Karamar hukumar Makoda.

Sarki ya Gargadi Sabon Dagaci da kada yayi hulda da bata gari, sannan ya horeshi da ya rika Sanar da Jami’an tsaro na duk wata bakuwar fuska daba a yarda da itaba ga hukumomin tsaro, ya kuma zama mai yin sulhu ga Talakawansa.

Alh Nasir Ado Bayero ya kuma horin Dagaci na Tangaji da yasa ido wajan gani yara na zuwa Makaranta da hada kai da Jami’am lafiya wajan yin Riga kafi Cuturcuka.