Daga Aisha Aliyu Umar
Allah ya yiwa jarumi a masana’antar kannywood Umar Malumfashi Wanda akafi sani da Bankaura ko Kafi Gwamna a yau din nan.
Umar Yahaya Mununfashi na daya daga cikin Iyaye Jarumai da suke bada muhimmiyar gudunmawa a Masana’antar Kannywood.
Ya fara harkar fim ne tun daga wasan dabe (Stage Drama) zuwa Television har Home Video (Kannywood) Sannan Babban Ma’aikaci ne A Nigerian Customs Service.
Darakta a masana’antar kannywood Falalu A Dorayi shi ne ya tabbatar da rasuwan Malam umar malumfashi a sahihin safinsa na Facebook.
Kafin rasuwarsa dai ya taka rawa a wani film mai dogon zango mai suna Kwana chasa’in wanda ake nunawa a tashar Arewa24 ,Inda ya fito a matsayin kafin Gwamna.
Marigayin dai ya shafe tsahon lokaci yana rashi lafiya.
Allah Yai masa gafara ya bawa iyaye da iyalai da Yan uwa hakurin rashinsa. Idan mutuwar tazo Allah kasa mu cika da imani.