NFF ta karawa kwamishinoni wasanni alawus na kaso 25 a gasar wasanni ta bana – Ibrahim Gusau

Date:

Daga Zainab Kabir Kundila

 

Hukumar kwallon kafa ta kasa ta bukaci kwamishinonin wasanni da a koda Yaushe su kasance masu gaskiya da adalci a yayin gudanar da ayyukan su.

Shugaban hukumar, Alhaji Ibrahim musa Gusau shine yayi kiran ne a yayin da yake bude taron horarwa na wuni Guda da aka tura shiryawa kwamishinonin da zasu jagoranci gasar cin kofin kwararu ajin maza Dana mata na kakar wasanni ta 2023 zuwa 2024 Wanda aka gudanar a nan jihar kano.

Talla

 

Alhaji Ibrahim musa Gusau yace Duk wani kwamishinan da aka samu da saba ka’idar gudanar da aiki ba za’a sassauta masa ba.

Ya bayyana rashin Jin dadi kan yadda aka samu karancin wadanda suka halarci taron daga jahohin arewancin kasar nan goma sha Tara da kuma abuja.

Tarihin Yadda Aka Fara Amfani da Kudade a Nigeria

Yace rashin halartar taron ka iya kawo fuskatar hukuncin rashin zama kwamishinan wasanni na wannan shekarar.

Shugaban yace hukumar kwallon kafa ta karawa kwamishinoni wasanni alawus alawus na kaso 25 a gasar wasanni ta wannan shekarar.

A nasa jawabin shugaba bada Alkalan wasanni na hukumar, Alhaji Babangida ya bukaci su suyi Aiki da abunda suka koya a yayin horon da aka basu.

Talla

A nasa jawabin Shugaban kungiya kwallon kafa ta jihar Kano, Alhaji Rabi’u Sharfi Ahlan ya godewa hukumar bisa zabar jihar Kano a matsayin jihar da za’a bada horan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...