Daga Auwal Alhassan kademi
An nada kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba a matsayin kakakin kwamitin yakin neman zaben Gawauna/Garo dake takarar gwamnan kano a jam’iyyar APC.
Muhd Garba wanda ya taba zama sakataren yada labarai na mataimakin kakakin majalisar wakilai a shekarar 1993 da kuma mataimakin gwamnan jihar Kano daga 1999-2003, dan jarida ne Wanda ya yi suna a duniya.
An nada shi Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu a shekarar 2015 a lokacin mulkin Ganduje na farko sannan ya sake nada shi Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida a 2019.
Cikin sanarwar da babban sakataren yada labaran gwamna Malam Abba Anwar ya aikowa kadaura24, yace nadin dai ya yi la’akari da shekaru da dama da Muhd Garba ya yi a matsayin kwararren dan jarida, kuma mai kare kimar mai gidansa a matsayin mai magana da yawun gwamnatin jihar Kano tun daga shekarar 2015.
Kwamishinan yada labaran baya ga kasancewarsa kwararren dan jarida, ya taba zama shugaban kungiyar Yan jarida ta Nigeria NUJ, sannan ya rike shugabancin kungiyar yan jaridu na africa ta yamma (WAJA) har karo biyu.
Har ila yau, ya rike mukamai da dama a kungiyoyi da kamfanoni daban-daban kuma har yanzu yana da kyakyawar alaka da yan jaridun da suke gudanar da aiki ba a jihar kano kadai ba har da kasa baki daya.
Tun lokacin da aka nada shi Kwamishinan Yada Labarai a shekarar 2015, yana tafiyar da harkokin yada labarai da huldar kafafen yada labarai na gwamnati da wadanda ba na gwamnati ba, ba wai kawai ya tabbatar da daidaiton masana’antu ba har ma da kyakkyawar dangantakar aiki.
Nadin ya fara aiki nan take Kuma zai jagoranci harkokin yada labarai da hulda da jama’a na kwamitin yakin neman zaben gwamna na 2023 a jihar kano.
Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Malam Garba Yusuf Abubakar, shi ne zai yiwa muhd garba Mataimaki, wanda ya taba rike mukamin kwamishina daban-daban a ma’aikatun yada Labarai 2003-2005, Tsare-tsare Kasa da Jiki 2005-2006, Muhalli, 2006-2010, ya taba zama Daraktan Yada Labarai, Shekarau 2003/2007.
Nadin yana tare da sakamako nan take. Hakan dai ya samo asali ne bisa shawarar dan takarar da kuma kwamitin yakin neman zaben, kuma shugaban jam’iyyar APC na jihar da gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne suka amince da shi.