DAGA BABANGIDA SANUSI KANO.
Aranar Alhamis ne kungiyar dikko sport light takaiwa manajan hukumar zirga zirga tashar mota mallakatar gwamnati jihar Katsina Alhaji Haruna Musa Rugoji ziyara, karkashin jagoranci shugabanta Tsohon Dan takarar majalisa karamar hukumar Batsari Hon Manusr Garba Rumah .
Da ya ke jawabi lokacin ziyarar shugaban kungiyar Hon. Mansur Garba Ruma yace duba da irin gudunmuwar da shugaban hukumar yake badawa ga al’umma ya basu damar bashi uban tafiya wannan kungiya.
Rumah ya kuma bayyana cewa zuwan Rugoji hukumar yasa hukumar tafarfado daga halin mutu kwai-kwai rai kwai-kwai data tsinci kanta, haka Kuma yana ganin shugowar manajan na KTSTA zai karawa tafiyar wani ginshiki da zai taimaka wajen tafiyar.
Sannan ya bayyana kungiyar da take fadakarwa kan jama’a su zabi dantakatar gwamnan jihar Katsina karkashin inuwar jam’iyyar APC a zabe Mai zuwa, Rugoji nada rawar takawa a wannan tafiya dan cigaban jihar Katsina ne gabansa.
Shi ma anasa jawabin Haruna Musa Rugoji yayi matukar godiya bisa wannan mukami da suka bashi,inda yayi alkawalin aiki tukuru dan samar da nasara a wannan tafiya.
Shugaban kungiyar dai ya samu rakiyar wasu daga cikin jigan-jigan kungiyar yayin ziyarar.