Daga Isa Ahmad Getso
Majalisar zartarwa ta jihar kano ta Kara kudaden gudanarwa ga masarutun Jihar Kano guda 5 domin cigaba da aiki.
Kwamishinan yada labarai na Jihar kwamared Muhammad Garba, ne ya bayyana hakan yau, yayin da yake yiwa Yan manema labarai karin haske kan yadda zaman majalisar zartar wa ta aiwatar a zamanta daya gudana jiya karkashin jagoranci gwamna Abdullahi Ganduje a gidan gwamnatin jaha.
‘Yan sanda sun kama guda cikin wadanda ake zargi da kisan dan Kabiru Gaya
Muhammad Garba, yace duba da yawan al’umma da sauran nauye nauyen dake Kan majalisar masarautar Kano gwamnatin ta rubanya alawus din masarautar daga miliyan hamsin zuwa miliyan dari.
- ” Su Kuma sauran Masarautun guda hudu wadanda suka haɗa da Bichi, Rano Karaye da Gaya an Kara musu daga Naira Miliyan 20 ya koma Naira Miliyan 40 domin inganta aiyukan su”. Inji kwamishinan
Ban janye daga takarar majalisar tarayyar Gezawa da Gabasawa ba – ‘Yar takarar PDP
Muhammad Garba yace majalisar zartarwar ta amince da fitar da naira miliyan dari Uku da hudu domin biyan alawus na malama dari biyu da tamanin da bakwai na jami’ar Yusuf tama sule.

Ya kara da cewa majalisar ta sahale za’a baiwa jami’ar kimiyya da fasata ta wudil Naira miliyan tamanin da hudu domin biyan alawus na malaman jami’ar.
kwamishinan yace gwamnatin ta kafa wani kwamiti, da zai yi duba Kan gine ginen rukunin gidajen Shiekh isiyaka Rabiu dana Shiekh Nasiru kabara dana Shiekh ja’afar domin gano matsalolin da suka hana masu gidajen tarewa.