Inganta Muhalli: Wata kungiya a Gwagwarwa ta yi feshin magani Sauro Gida-gida

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

 

Wata kungiya mai suna “Mu taimaki juna” dake garin Gwagwarwa a karamar hukumar Nasarawa Kano ta gudanar da aikin feshin magani Sauro a unguwar a wani matakin na takaita yaduwar cutar zazzabi cizon Sauro a Kano.

 

Jim kadan bayan kammala aikin feshin a zantawarsa da wakilin Kadaura24, Shugaban kungiyar Com. Abubakar Idris Gwagwarwa, yace sun gudanar da aikin ne domin magance matsalar zazzabin cizon saura da ya addabi al’umma a wannan lokaci.

 

Yace dama duk shekara sukan gudanar da aikin, Inda suke shiga lungu da sako na yankin tare da shiga Gida-gida don yin feshi a bandakuna domin kashe duk wasu sauraye dake cutar da al’umma.

Talla

” Mun kirkiri wannan kungiya ne ta “mu taimaki juna” saboda mu rika gudanar da irin wadannan aiyuka don inganta Muhallanmu da Kuma taimakawa junanmu, saboda idan muka ce komai sai gwamnati ta yi mana to Zamu dade cikin matsaloli”. Inji Abubakar Idris

 

Shugaban kungiyar ya kuma kara da cewa su kan sayi magani cutar zazzabin cizon saura don rabawa ga marasa karfi dake yankin, sannan yace su kan share Kuma su kwashe shara a magudanan ruwa.

 

Talla

” Yadda mukai wannan aikin a Wani yanki na Gwagwarwa Muna sa ran nan gaba zamu Kara fadada aikin zuwa dukkanin unguwannin dake karkashin garin dagaci Gwagwarwa, don bada misali ga saura. Matasa don suma su yi koyi”.

 

 

Yace karo-karo su ke yi don tara kudaden da suke sayo kayan da suke aikin da su, don haka ya bukaci Masu rike da mukaman gwamnati da masu hannu da shuni da su rika tallafawa kungiyoyi irin nasu don ciyar da al’umma gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Kotu ta aike da Matashin dake shigar mata a Tiktok da film gidan gyari

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab'i...

Rabon Jakai: Faizu Alfindiki ya aikawa Sanusi Bature budaddiyar wasika

Zuwa ga: DG. Sunusi Bature Dawakin Tofa Daraktan Yada Labarai, Gwamnatin...

Dama ba mu yi shirin yin hawan babbar Sallah ba – Sarki Aminu Ado Bayero ya fadi dalili

Daga Isa Ahmad Getso   Sarkin Kano na 15 Aminu Ado...

Abdullahi Muhammad ya zama sabon shugaban kungiyar NUJ Pyramid Radio

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Mai rikon mukamin shugaban kungiyar yan...