Matasa sun hallaka wani barawon babura da ya addabi yankin Gwarzo Zuwa Dayi

Date:

Daga Kabiru Muhammad Getso

 

Wasu Mutane a karamar hukumar Gwarzo sun halaka wani barawon babura da ya addabi yankin Gwarzo zuwa dayi.

 

Barawon kafin rasuwarsa yayi yunkurin karbe babur din wani a wata hanya kusa da garin kwantara, inda ya buge mai babur din kuma ya amshe babur din ya barshi a nan kwance.

 

Sai dai bayan da shi mai babur din ya samu kansa, sai ya kira waya ga wasu a can gaba inda suka yiwa barawon tara-tara, suka tare shi, suka kuma farmasa  har sai yace ga garinku nan.

 

Talla

Barawon Magidanci ne da akai hasashen yakai kimanin Shekaru hamsin, an same shi da wata hoda mai bugar da mutane da kuma wasu kudade, tuni aka garzaya da shi Sashin adana gawawwaki dake Babban Asibitin Gwarzo.

 

Talla

Wakilin kadaura24 ya tuntubi Jam’in hudda da Jama’a na rundunan yan sandan jihar Kano Abdullahi Haruna kiyawa wanda yace bai Sami labarin faruwar lamarin ba, Inda yace da zarar ya gama bibiyar lamarin zai yi mana karin bayani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dan Majalisar tarayya daga Kano ya fice daga jam’iyyar NNPP

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kano Municipal, Injiniya Sagir...

Abin mamaki: Barawo ya sace Motar dake cikin ayarin motocin gidan gwamnatin Kano

Wani barawon mota ya kutsa cikin gidan gwamnatin jihar...

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...