Daga Rukayya Abdullahi Maida
Sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa a gidan haya yake zaune a Abuja, Inda yace yana Addu’ar Allah ba bashi damar gina nashi gidan a Abuja
Tsohon Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga wasu rahotanni dake cewa an ba shi dala miliyan 1 domin ya bar jam’iyya NNPP.
Ban ce zan mika ragamar jami’o’i ga jihohi -Atiku Abubakar
Rahotannin sun nuna cewa Malam Shekarau ya karbi kudin ne domin ya mara baya ga wanda ake zargin ya bada kudin idan Shekarau ya fice daga jam’iyyar NNPP.
Ya kara da cewa: “Ba wai ba ma son kudi ba, amma mutuncinmu ya fi wata dukiya muhimmanci. Duk wanda ya san wani gida a wajen gidan da aka gina mani bisa yarjejeniyar fansho, na bar masa”.
“Wannan hannun da kuke gani babu approval din da bai bayar ba,don haka ina so Mutane su Sani ni mutunci yafi kudi a waje na”. Inji Shekarau
Malam Ibrahim Shekarau yace duk wani al’amari da zai yi mutuminsa yake fara kallo kafin komai don cika Umarnin addini na kare mutuncin fiye da komai.