Hajjin bana: Rukuni na biyu na Maniyatan jihar Kano sun tashi zuwa kasa mai tsarki

Date:

Daga Zara Jamil Isa

 

Rukuni na biyu na Maniyatan jihar Kano sun tashi daga filin jirgin saman Aminu Kano zuwa birnin Madina na kasar Saudiyya.

 

Sakataren zartarwa na hukumar Alhaji Mohammad Abba Danbatta ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a Kano.

 

Ya ce wadanda aka kwaso a zango na biyu sun hada da mahajjata daga karamar hukumar Fagge, ma’aikatan hukumar, malamai, da sauran jami’an hukumar.

 

Mohammad Abba Danbatta ya lura cewa jirgin ya tashi ne da misalin karfe 8 na safiyar yau Alhamis.

 

Da yake jawabi ga mahajjatan kafin tafiyarsu, sakataren zartaswar ya umarce su da su kasance jakadu nagari tare da yi musu addu’ar samun zaman lafiya a jihar Kano da kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kansila a K/H Garum Mallam ya rabawa marayu 300 kayan Sallah

Daga Safiyanu Dantala Jobawa   Sama da yara mayaru 300 ne...

Sallah: Baffa Babba ya raba buhu 2,000 na Shinkafa ga Kungiyoyin Tinubu a Kano

Babban daraktan cibiyar kula da ingantuwar aiyuka ta kasa...

Babbar Sallah : Kansilan Lajawa ya raba Naira dubu 500 ga al’ummar mazabarsa

Daga Nura Adam   Kansilan mazabar Lajawa a karamar hukumar Wudil...