Majalisar dattijai ta amince da mutanen da Buhari ke son naɗawa Ministoci

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

Majalisar dattijan Najeriya ta amince da sabbin ministoci bakwai da shugaba Muhammadu Buhari ya tura ma ta domin tabbatar da naɗinsu.

 

An tabbatar da naɗin ne bayan zaman tantace su da majalisar ta yi a zamanta na wannan Larabar.

 

Yayinda wasu daga cikin sabbin ministocin, musamman tsohon ɗan majalisa, da aka bukaci su yi gaisuwar majalisa su wuce, wasu daga cikinsu an tsare su da tambayoyi kan abubuwan da ya shafi kasa.

 

Shugaba Buhari, a wata wasika da ya aikewa majalisa mai dauke da kwanan watan 15 ga watan Yuni, 2022, ya bukaci majalisar ta amince da naɗinsa.

 

Ya ce neman bukatar amincewa da naɗin ya yi daidai da tanadin kudin tsarin mulki sashi na 147(2) na kudin tsarin mulkin shekara ta 1999 na Tarayyar Najeriya, da aka yiwa kwaskwarima.

 

Ministocin da aka tabbatar da naɗin nasu sun haɗa da: Henry Ikechukwu Ikoh – daga Abia; Umana Okon Umana – daga Akwa Ibom; Ekumankama Joseph Nkama- daga Ebonyi; da Goodluck Nanah Opiah – daga Imo.

 

Sauran su ne Umar Ibrahim El-Yakub – daga Kano; Ademola Adewole Adegoroye – daga Ondo; da Odum Udi – daga Rivers.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sallah: Baffa Babba ya raba buhu 2,000 na Shinkafa ga Kungiyoyin Tinubu a Kano

Babban daraktan cibiyar kula da ingantuwar aiyuka ta kasa...

Babbar Sallah : Kansilan Lajawa ya raba Naira dubu 500 ga al’ummar mazabarsa

Daga Nura Adam   Kansilan mazabar Lajawa a karamar hukumar Wudil...

Da dumi-dumi: Kotu ta aike da Matashin dake shigar mata a Tiktok da film gidan gyari

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab'i...