Daga Zara Jamil Isa
Hukumomi a kasar saudiyya sun tabbatar da ganin jinjinrin watan Zul Hijjah wanda a Cikin sa ne ake gudanar da Ibadan aikin Hajji.
Sanarwar da Haramain Sharifain ta fitar tace gobe alhamis ita ce daya ga wata kuma za’a gudanar da Arafat a ranar juma’ar 8 ga watan Yuli na shekarar 2022.
Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa za’a gudanar da idin babbar sallah a ranar asabar 9 ga watan Yuli na shekarar 2022.