Daga Halima Musa Abubakar
Uwar jam’iyyar APC ta Kasa ta turo Kwamitin karbar korafe-korafe Kan zaben fidda gwani na kujerar Gwamnan Jihar Kano wanda aka gudanar Ranar alhamis din data gabata.
Kadaura24 ta rawaito yayin da yake ganawa da manena labarai a sakatariyar jam’iyyar APC ta Kano Shugaban Kwamitin Dr. Anthony Macfoy yace an turo su kano ne domin karbar duk wani korafi da ya shafi zaben fidda gwanin.
Dr. Macfoy ta Bakin sakatariyar Kwamitin Hajiya Bilksu M Kay-kya yace zasu Kwashe kwanaki 7 Suna Zama daga yau asabar domin tattara Rahotannin korafe-korafen ‘ya’yan jam’iyyar musamman Waɗanda Suka shiga zaben dama Waɗanda basu shiga zaben ba.
” Shugaban jam’iyyar APC na Kasa Sanata Abdullahi Adamu ne da hadin gwiwar Kwamitin amintattu na Jam’iyyar suka turo mu kano domin mu saurara ko mu karɓi korafi akan zaben da akai”inji Hajiya Bilksu
Da take karin bayani kan abun sakatariyar Kwamitin Hajiya Bilkisu kai-kai tace zasu Kwashe kwanaki 7 Suna Zama tun daga 10 na safe har zuwa karfe 5 na yamma.
Bilksu Kai Kai ta Kuma buƙaci hadin Kan ‘ya’yan jam’iyyar APC na Jihar Kano domin su sami kyakykyawan yanayi da zasu gudanar da aiyukan su kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC ya dora musu.
Kwamitin Mai Mutane uku yana karkashin Shugabancin Dr. Anthony Macfoy sai sakatariyar Kwamitin Hajiya Bilksu M kay-kay da Kuma mamba Alhaji Ibrahim Shehu