Ƴan takarar shugaban ƙasa da ke fafatawa a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar PDP na gabatar da jawabi ga wakilan jam’iyyar da za su fitar da gwani daga cikinsu.
A cikin jawabinsa Atiku Abubakar ya ce PDP a shirye take ta ciyar da Najeriya gaba.
“Wannan taron shi ne na ƙarshe a zamanin mulkin APC”, in ji Atiku.
A cikin jawabinsa kuma ɗan takara Dr Nwachukwu Anakwenze ya sanar da janye takararsa ta shugaban ƙasa.
Tsohon shugaban majalisar dattijai kuma tsohon sakataren gwamnati Anyim Pius Anyim ya ce zai samar da ci gaba a Najeriya tare da haɗa kan ƴan ƙasa