Daga Junaidu Sani
Guda cikin yan takarar gwamna a jam’iyy APC kuma Sanata mai wakiltar mazabar Kebbi ta arewa, Dr Yahaya Abdullahi yayi fatali da zaben fidda gwani na gwamnan jihar Kebbi na jam’iyyar APC da aka gudanar a ranar Alhamis 26 ga watan Mayu 2022 a Birnin Kebbi.
A wata sanarwa dauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Muhammad Jamilu Yusuf Gulma ya bayyana yadda zaben ya gudana a matsayin wasan yara, inda ya yi zargin cewa shugabannin kananan hukumomi ne suka tsaya kan akwatunan zabe Suna rubutawa delegate tare da sunayen ‘yan takarar .
Kadaura24 ta rawaito Sanarwar ta bayyana yadda zaben ya gudana a matsayin wanda bai dace da tsarin demokradiyya da siyasa ba.
Don haka aka yi kira ga dukkan magoya bayan Sanata Yahaya Abdullahi da su kwantar da hankalinsu a matsayinsu na ‘yan kasa masu bin doka da oda domin daukar mataki na gaba.
Idan za a iya tunawa sakamakon zaben fidda gwani na gwamna da aka kammala a jihar Kebbi ya nuna cewa Dr Nasiru Idres Kauran Gwandu ya samu kuri’u 1055 yayin da Abubakar Gari Malam ya samu kuri’u 35 yayin da Sanata Yahaya Abdullahi Mallamawan bai Sami kuri’a ko daya ba.