Babbar Kotun Tarayyar Najeriya da ke zama a Yenegoa babban birnin Bayelsa ta yanke hukuncin cewa tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan zai iya takarar shugabancin ƙasar
Jaridun Najeriya sun ruwaito cewa alkali mai shari’a Isa Hamma Dashen ne ya yanke wannnan hukunci a ranar Juma’a.
Sai dai har zuwa yanzu Jonathan bai fitar da wata sanarwa ba da ke nuna cewa zai tsaya takara.
Ko a kwanakin baya sai da gamayyar kungiyoyi a arewacin Najeriya suka saya wa Jonathan tikitin takarar shugaban kasa karkashin Jam’iyyar APC, duk da cewa Jonathan ɗin ya nesantar da kansa daga tikitin.