Daga Sayyadi Abubakar Sadeeq
A shirye-shiryenta na tunkarar aikin Hajjin 2022, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta ce ta samu masaukin maniyatan ta a unguwar da ke kusa da Harami a birnin Makkah na kasar Saudiyya .
Sakataren zartarwa na hukumar Muhammad Abba Dambatta ne ya bayyana hakan a wata zantawa da manema labarai domin shaidawa ‘yan jaridu shirye-shiryen da suke yi don samun Nasarar aikin Hajjin bana.
Muhammad Abba Dambatta wanda ya dawo Najeriya daga kasar Mai tsarki a ranar alhamis ya ce “Hukumar ta tanadi masauki a kusa da Harami, domin saukakawa alhazan jihar don su sami damar ziyartar babban Masallacin Haramin Makka ba tare da sun wahala ba”.
A cewarsa, gwamnatin jihar ta yi amfani da mafi yawan gidajen da aka kama, yayin da aka kara da wasu sabbi saboda ba su wuce shekaru hudu zuwa biyar ba.
Ya bayyana cewa ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta sanya dokar ba da tazara tsakanin mahajjata da akalla mita 4.
Dangane da batun ciyarwa, Muhd Dambatta ya bayyana cewa hukumar ta kulla yarjejeniya da wani kamfani na samar da abinci ga alhazan jihar Kano, inda ya kara da cewa a baya hukumar ta yi aiki da kamfanin kuma ta ji dadin yadda suka gudanar da aikin ciyar da mahajjatan.
“Ciyar da abinci a Masha’ir a halin yanzu hukumomin Saudiyya sun karbe ragamar sa, sabanin yadda ake yi a baya, inda aikin da ya rataya a wuyan hukumar alhazai ta jihar yanzu, Saudiyya ce za ta ba da abinci ga mahajjata a duk tsawon lokacin Masha’ir,” in ji Dambatta.
Ya kara da cewa kowane mahajjaci zai biya kudi sama da N500,000 domin na abinchi a ciyar Masha’ir.
“Amma, mun kokawa hukumomin da abun ya shafa cewa muna da alhazai masu fama da rashin lafiya wadanda ba za su iya cin abincin da ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya za ta bayar ba.
“Sun yi mana alƙawarin cewa za su tattauna kan koke-kokenmu kuma za su yi abin da ya kamata,” in ji Sakataren Zartarwar.
Duka dai a shirin kyautatawa mahajjatan, Danbatta yace hukumar ta yi shirin samar da Masallacin Juma’a a sansanin alhazai na Jihar Kano, tare da gyaran bandakunan maza da mata na dake cikin sannanin.
Kadaura24 ta ziyarci sansanin Kuma ta iske Iska ta dage wasu daga cikin kwanan rufin runfunan da mahajjata suke zama, sai dai sakataren zartarwar yace tuni gwamna Ganduje ya bada Umarnin Fara aikin gyara runfunan gabanin fara jigilar maniyata aikin Hajjin bana.
Dambatta ya kuma bayyana cewa nan ba da dadewa ba za a bayyana hakikanin kudin aikin Hajjin bana, inda ya ce za a tantance shi ne ta hanyar kudaden da ake kashewa a bangaren gida da kuma Masha’ir.