Kadaura24 ta rawaito cewa, Kawu Sumaila ya bayyana haka ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook yau dinnan, inda ya rubuta kamar haka “Godiya Ta tabbata ga Allah mamallakin mulki, zamana a jamiyyar APC yazo karshe, Wanda duk yake ganin rashin hakuri na ya rage nasa, ina yiwa kowa fatan Alkhairi.”

Kawu Sumaila dai tuni ya bayyana cewa sun zauna da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, kuma sun daidaita, abinda ya alamta cewa da alama Kawu zai fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari anan kusa.

Kawu Sumaila dai ya nemi kujerar Sanatan kano ta kudu a jam’iyyar APC tun shekara ta 2019 har wannann lokaci da ya sauya Sheka bisa zargin ba za a yi masa adalci ba.

Tuni dai jam’iyyar NNPP tayi nisa wajen karbar baki daga jam’iyyu musamman ma APC a jihar Kano, inda tuni yan majalisun tarayya guda biyu dana majalisar dokokin jiha guda uku suka shiga jam’iyyar, baya ga yunkurin da ake ganin cewa tawagar nan ta G7 karkashin jagorancin Sanata Malam Ibrahim Shekarau na gab da shiga jam’iyyar.