Tunda Musa Iliyasu Kwankwaso ya kama aiki yan APC a Kano kowa zai sha romon dimokaradiyya – Dini Falalu Fagge

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Guda cikin ya’yan jam’iyyar APC a jihar Kano Hon. Dini Falalu Fagge ya bukaci dakkanin yan jam’iyyar APC a jihar Kano da su kwantar da hankulansu tunda Musa Iliyasu Kwankwaso ya shiga ofis kowa zai sharbi romon dimokaradiyya.

Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito tun a shekarar da ta gabata Shugaban Kasa Bola Tinubu ya baiwa Musa Iliyasu Kwankwaso mukamin babban daraktan kudi na hukumar raya kogunan Hadeja-Jama’are, sai dai a wancan lokaci sai jiya juma’a ya karbi takardar shaidar kama Aiki.

InShot 20250309 102403344
Talla

” Kowa ya san Musa Iliyasu Kwankwaso mutum ne da ya saba taimakawa yan jam’iyya ko da ba shi da mukami ballantana yanzu da ya sami babban mukami a gwamnatinsa tarayya, don haka kowa ya riya shan romon dimokaradiyya”.

Dini Falalu Fagge ya bayyana hakan yayin wata ganawa ta musamman da ya yi da jaridar Kadaura24 ranar asabar.

Ya ce Musa Iliyasu Kwankwaso zai yi aiki tukuru don taimakawa harkokin noma a jihohin Kano Jigawa da Bauchi.

Dini Falalu Fagge wanda yake guda ne cikin makusantan Musa Iliyasu ya kara da cewa ” mun fahimci madugun Kwankwasiyya bai iya rabawa mutanensa kayan azumi ba, to ya sani Musa Iliyasu Kwankwaso zai ba shi gona don ya rika noman abun da zai rika taimakawa mutane.

Kisan Edo: Yansanda sun bayyana adadin mutanen da suka kama

Da yake mayar da martani ga yan adawa Dini Falalu Fagge ya ce Musa Iliyasu Kwankwaso ya yarda da cewa Allah ne mai yi shi yasa yake samin nasara, ba irin su Abubakar Rano ba da suke dauka Kwankwaso ne mai iya yi wani komai.

Daga karshe Dini Falalu Fagge ya yiwa duk Manoman Kano Jigawa da Bauchi albishir na cewa za su sami tallafin aikin noma kala-kala daga Hukumar raya kogunan Hadeja-Jama’are ta hannun babban daraktan kudi na hukumar Musa Iliyasu Kwankwaso.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...