Gwamnatin Kano ta yi Allah -wadai da kisan killar da aka yi wa mafarauta a Edo

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Gwamnatin jihar Kano ta yi Allah -wadai da kisan killar da aka yiwa wasu mafarauta yan asalin jihar a hanyarsu ta dawowa gida a jihar Edo.

“Gwamnatin jihar Kano ta jajantawa iyalai da abokanan wadanda suka mutu a wannan mummunan lamari da ya faru a garin Uromi na jihar Edo. Mummunan kisan da ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 16, Wannan wani mummunan aiki ne da ya zama wajibi a dauki matakin hukunta duk wanda aka samu da hannu a ciki”.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya sanyawa hannu kuma aka aikowa Kadaura24.

InShot 20250309 102403344
Talla

Rahotan sun nuni da cewa mafarautan da wasu matasa dake dauke da makamai sun yi wa wadanda lamarin ya rutsa da su kwantan bauna a hanyarsu ta dawowa gida jihar Ribas zuwa Kano domin gudanar da bukukuwan Sallah.

Ya ce ” Wannan tashin hankalin wani abin takaici ne ga iyalan wadanda abin ya shafa ba, kuma akwai bukatar daukar matakai don ganin hakan na ta sake faruwa ba.

“Bisa la’akari da wadannan abubuwan da suka faru, muna kira da a gudanar da bincike cikin gaggawa, kuma dole ne a gurfanar da duk wadanda aka samu da hannu a wannan ta’asa, ciki har da jami’an tsaro da suka yi sakaci da aikinsu”. Inji Waiya

Sallah: Kungiyar RATTAWU a Kano ta sauke kabakin arziki ga ya’yanta

Sanarwar ta ce Hukumomin Najeriya ya kamata su tuna da irin nauyin da ya rataya a wuyansu a karkashin dokokin kasa da kasa na kare hakki da rayukan dukkan β€˜yan kasa, tare da tabbatar da cewa ba a sami wata cutarwa ga kowa ba in kuma an sami wanda yayi to a hukunta shi.

Muna kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da Gwamna Monday Okpebholo da su yi Allah-wadai da wannan aika-aika tare da jajircewa wajen tabbatar da adalci wajen ganin an gaggauta gurfanar da wadanda suka aikata laifin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related