Zargin bata suna: Wata Kotu a Kano ta aike da Danbilki kwamanda gidan gyaran hali

Date:

Daga Umar Usman Sani Mainagge
An gurfanar da Abdulmajid Danbilki kwamanda a gaban kotu majistry Mai lamba 58 karkashin ai sharia Aminu Gabari.
Ana dai zargin Danbilki da laifin Bata suna da kalaman batanci da yunkurin tayar da hankali, yayin wata hira da yayi a Wani gidan Radio, yayi batanci ga gwamnan jihar Kano da zargin baiwa Mai mala buni cin hanci
Sai dai Danbilki kwamanda ya musanta dukkanin laifukan da ake zargin ya aikata Waɗanda Suka hadar da 1. Bata suna
2. furta kalaman kaskanci
3. yunkurin tayar da hankali.
Lauyan gwamnati Barr. Wada A Wada ya shedawa kotu cewa tun da Wanda ake zargi ya musanta zargin Suna rokon wata Rana domin kawo shedunsu a gaban kotun.
Barr wada a wada Yayi rokin da a umarci yansanda su kawo kundin bayansu na bincike akan Wanda ake Kara .
Lauyan Abdulmajid Danbilki kwamanda a gaban kotu Barr. Ibrahim chedi yayi rokon da a Sanya Wanda yake kare a hannun belli kuma zasu tabbatar da cika dukkanin wasu ka’idojin da kotu ta jindaya .
Mai shari’a Aminu Mahd  Gabari ya yi umarni ga mai gabatar da Kara da ya kawowa kotu Shedu.
Kuma anyi umarni da a ajiyeshi a gidan gyaran Hali zuwa Ranar 15

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Malam Ibrahim Khalil ya ba da fatawa kan Sallar Juma’a a ranar Idi

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban majalisar Malamai ta Arewacin Najeriya,...

Da dumi-dumi: Sarki Sanusi Fadi Matsayarsa Kan Hawan Sallah Babba

Daga Sani idris Mai waya   Mai Martaba Sarkin Kano na...

Sallah: Shugaban K/H Rano ya gargadi matasan yankin kan zaman lafiya

Daga Isa Ahmad Getso   Shugaban karamar hukumar Rano Malam Naziru...

Kansila a K/H Garum Mallam ya rabawa marayu 300 kayan Sallah

Daga Safiyanu Dantala Jobawa   Sama da yara mayaru 300 ne...