Kotu ta yi fatali da roƙon Muhuyi Magaji na kotu ta hana ƴan sanda su kama shi

Date:

Babbar Kotun Taraiya a Jihar Kano ta yi fatali da buƙatar da dakataccen Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado.

A roƙon da ya shigar gaban kotun, Riminga ya nemi kotun da ta hana kwamitin bincike da majalisar dokoki ta Kano ta kafa, da kuma hana ƴan sanda su bincike shi, tsare shi ko yi masa barazana.

Sannan ya roƙi kotun da ta bada umarnin kowa ya dakata ba tare da ɗaukar mataki kan takardun shaidar lafiya na biyu da a ke zargin yayi amfani da su.

Da ta ke yanke ƙwarya-ƙwaryan hukunci a yau Talata, Mai Shari’a Jane Inyang, ta ce kwamitin bincike da aka kafa da kuma jami’an tsaro suna da iko da doka ta basu na su binciki Rimingado.

Inyang ta kuma yanke cewa babu hurumi na jaddada ko yin watsi da hukuncin da kotu mai hurumi iri ɗaya ta yi da wacce a ka miƙa wa ƙorafi ta yi.

Ta kuma ce kamata ya yi Rimingado ya shigar da ƙorafi a kan yan majalisar dokoki a Babbar Kotun Jiha ba ta taraiya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Amfani da al’ada a cikin fina-finan kannywood ne ya hana masa’antar ci gaba – Khadija Osi

Jaruma a masana'antar Kannywood Khadija Muhammad wacce aka fi...

Nasarar da Ɗaliban Kano suka Samu a NECO Kokari ne na Gwamnatin Ganduje – Sanusi Kiru

Tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Hon. Muhammad Sanusi...

Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Aikin samar da wutar sola na Naira Biliyan 12 a asibitin Malam Aminu Kano

Kwana biyu bayan rikicin wutar lantarki tsakanin Asibitin Koyarwa...

Kano Ta Zama Zakara A Jarrabawa NECO Ta Bana

Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta Najeriya (NECO),ta fitar...