Kotu ta yi fatali da roƙon Muhuyi Magaji na kotu ta hana ƴan sanda su kama shi

Date:

Babbar Kotun Taraiya a Jihar Kano ta yi fatali da buƙatar da dakataccen Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado.

A roƙon da ya shigar gaban kotun, Riminga ya nemi kotun da ta hana kwamitin bincike da majalisar dokoki ta Kano ta kafa, da kuma hana ƴan sanda su bincike shi, tsare shi ko yi masa barazana.

Sannan ya roƙi kotun da ta bada umarnin kowa ya dakata ba tare da ɗaukar mataki kan takardun shaidar lafiya na biyu da a ke zargin yayi amfani da su.

Da ta ke yanke ƙwarya-ƙwaryan hukunci a yau Talata, Mai Shari’a Jane Inyang, ta ce kwamitin bincike da aka kafa da kuma jami’an tsaro suna da iko da doka ta basu na su binciki Rimingado.

Inyang ta kuma yanke cewa babu hurumi na jaddada ko yin watsi da hukuncin da kotu mai hurumi iri ɗaya ta yi da wacce a ka miƙa wa ƙorafi ta yi.

Ta kuma ce kamata ya yi Rimingado ya shigar da ƙorafi a kan yan majalisar dokoki a Babbar Kotun Jiha ba ta taraiya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasan Kano biyu a Benue

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi...

Rashin Jami’ar Mallakin jihar a shiyyar Kano ta Arewa na kokarin bayar da yankin baya – Alh. Mustapha Ahmad Gwadabe

Daga Shehu Hussaini Ahmad Getso An bukaci Gwamnatin jihar Kano...

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Almuharram a Nigeria

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji...

Yan uwan wata mata sun zargi Asibitin Malam Aminu Kano da sakaci wajen mutuwar yar uwarsu

Daga Sadiya Muhammad Sabo   Yan uwan wata mata da ta...