Daga Khadija Abdullahi Umar
A ranar Talata ne majalisar dattawa ta kada kuri’ar yin gyare-gyare ga kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999 wanda ya baiwa majalisun jihohi da na shari’a da kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu a fannin kudi.
A kuri’ar da aka kada a zauren majalisar, ‘yan majalisar dattawa 83 ne suka kada kuri’ar amincewa da ‘yancin cin gashin kan harkokin kudi ga majalisun dokoki da na shari’a na Kananan Hukumomin, yayin da Sanata daya ya ki amincewa da hakan.
Sanatoci 92 ne suka kada kuri’ar amincewa da kudurin yin gyaran fuska ga ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomin, yayin da Sanatoci biyu suka ki amincewa.
Majalisar ta yi watsi da shirin sauya sunan karamar hukumar Barkin Ladi da ke jihar Filato zuwa Gwul.
A kuri’ar da aka kada, ‘yan majalisar dattawa 67 ne suka kada kuri’ar neman sauya suna, yayin da 28 suka ki amincewa.
Shawarar ta gaza cika kaso biyu bisa ukun da ake bukata.
Kafin Amincewa da kowane kudiri , dole ne ya samu rinjaye na kashi biyu bisa uku a zauren majalisar dattawa.