Daga Tijjani Mu’azu Aujara
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Birtaniya domin duba lafiyarsa wanda ake sa ran zai dauki tsawon kwanaki goma sha hudu.
Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasar, shi ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da yasa Mata hannu a ranar Talata, Inda ya ce shugaban zai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya a Kenya Gabanin ya wuce kasar ta burtaniya.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Adesina ya bayyana cewa shugaban kasar zai bar Abuja ranar Talata 1 ga watan Maris domin halartar bikin cika shekaru 50 da kafa Hukumar Kula da Muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya (UNEP@50), wanda aka shirya gudanarwa tsakanin 3 – 4 ga Maris, 2022 a Nairobi, Kenya, don girmama gayyatar da takwaransa na Kenya Uhuru Kenyatta ya yi masa.
Adesina ya ce Shugaba Buhari zai samu rakiyar Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, Karamin Ministan Muhalli, Sharon Ikeazor, Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Maj.Gen Babagana Monguno (rtd), Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa Hukumar, Amb. Ahmed Rufai Abubakar, da Shugabar Hukumar ‘Yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa.