Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar zabe na 2021 da aka yiwa gyara Kuma aka dade ana jira.
Shugaban ya rattaba hannu kan kudirin gyaran dokar da karfe 12:25 na rana a wani dan kwarya-kwarya biki da ya samu halartar shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan da kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da dai sauransu.
Ya ce dikar zaben da ya sanya wa hannu ta zo da babban ci gaba domin “zata ba da damar yin zabe Cikin gaskiya Kuma a bayyane.”
Sai dai Buhari ya bukaci majalisar kasar nan ta sake yin aiki ga dokar don ta haramta wa masu rike da mukaman siyasa shiga takara domin ya dace da kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya