NCAA ta karbi Koken da akai akan Kamfanin Air Peace na rashin girmama wa ga Sarkin Kano

Date:

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa
 Wani kawun Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya rubutawa hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya wasikar koke, inda ya nemi a hukunta kamfanin Air Peace saboda abin da ya kira da rashin girmama wa ga sarki da Mutanen Jihar Kano.
 A cikin koken da ya shigar gaban hukumar NCAA a jiya, kawun sarkin Wanda kuma daya daga cikin makusantan sa, Isa Sanusi Bayero, wanda aka fi sani da Isa Pilot, ya ce kamfanin jirgin ya jinkirta jigilar su daga Banjul zuwa Legas da sama da sa’a daya kuma ya hana su shiga jirgin da zai hada su zuwa Kano domin sun iso Legas saura minti 30 a tashi.
 Bayero ya ce, “Mu 10 ne har da Mai Martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da wasu fasinjojin na Musamman guda hudu tare da karin wasu fasinjoji masu guda biyar duk mun shiga jirgin Air Peace mai lamba P47776 da ya dawo daga Banjul zuwa Legas.
 “An shirya tashin mu daga Banjul da karfe 00:10 na safe a ranar 24 ga Fabrairu, 2022, amma mun tashi daga Banjul da karfe 01:19 na safe, muka sauka a Legas da karfe 5:45 na safe.  Da misalin karfe 6:15 jirginmu ya tashi zuwa Kano a dai jirgin na Air Peace”. Inji Isa pilot
 Ya ce shi da kan sa ya kirawo Shugaban Kamfanin na Air Peace, Allen Onyeama, domin ya sanar da shi halin da ake ciki, ya kuma bukace shi da ya taimaka ta hanyar jinkirta tashin su zuwa Kano, domin girmamawa ga mai martaba Sarkin Kano.
 “A fili yace yaki kuma ya sha alwashin cewa ba zai yi hakan ba.  Ni da kaina na dauki wannan a matsayin cin fuska da kuma rashin mutunta mai martaba shi da al’ummar Kano baki daya.” inji takardar korafin
 Ya ce, duk da cewa sun kama otal ne kudinsu, kamfanin jirgin ya kuma bukaci su biya kudin “No-show” a lokacin da suke son sake tsara yadda jirgin gaba na kamfanin da zai zo da karfe 7 na dare.
 “Wannan wani matsanancin hali ne na rashin hankali da rashin tausayi.  Dangane da abin da ya gabata, na ji matukar bacin rai kuma ina neman ku yi abun da ya dace don daukar matakan da suka dace don hana faruwar hakan a nan gaba.,” in ji shi.
 Da wakilin Jaridar Daily trust ya tuntubi mai magana da yawun kamfanin Inda ya ce zai binciki lamarin ,amma kuma har lokacin hada wannan rahoton bai tuntube shi ba.
 Darakta-Janar na NCAA, Kyaftin Musa Nuhu, ya tabbatar da samun wasikar koken amma ya ki cewa komai.
 “Zan iya cewa mun sami wasikar, Kuma muna aikin akan ta amma ba zan iya cewa komai a kai ba,” in ji shi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...