Dokar Zabe: Buhari ya ce wasu daga cikin tanadin Sabuwar dokar zabe za su inganta harkokin zaɓe

Date:

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya buƙaci Majalisun Dokokin ƙasar su goge sashen da ya hana masu muƙaman siyasa neman takara a cikin sabuwar dokar zaɓen da ya sanya wa hannu a yau Juma’a.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake sanya wa dokar hannu a fadarsa da ke Abuja.

Sashe na 84 (12) na Dokar Zaɓe ta 2022 ya buƙaci duk wani mai muƙamin siyasa ya ajiye muƙaminsa kafin ya tsaya wata takara a babban zaɓe.

Hakan na nufin za a tilasta wa wasu manyan ƙusoshin gwamnatin ta Buhari su sauka daga muƙamansu kafin babban zaɓe na 2023.

Buhari ya ce wasu daga cikin tanadin dokar za su haɓaka harkokin zaɓe “kamar 3, 9(2), 34, 41, 47, 84(9), (10), (11) da sauransu”.

“Sai dai abin ba haka yake ba… a sashe na 84 (12) wanda ya shatale masu riƙe da muƙaman siyasa game da zaɓensu da kuma jefa musu ƙuri’a a manyan tarukan jam’iyyu idan ba a gudanar da zaɓen ba cikin kwana 30 kafin zaɓe,” in ji shugaban.

Buhari ya shafe kusan kwana 25 kafin ya sanya wa dokar hannu, wadda ‘yan majalisar suka yi wa kwaskwarima sau biyu kafin ya amince da ita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...