Dokar Zabe: Buhari ya ce wasu daga cikin tanadin Sabuwar dokar zabe za su inganta harkokin zaɓe

Date:

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya buƙaci Majalisun Dokokin ƙasar su goge sashen da ya hana masu muƙaman siyasa neman takara a cikin sabuwar dokar zaɓen da ya sanya wa hannu a yau Juma’a.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake sanya wa dokar hannu a fadarsa da ke Abuja.

Sashe na 84 (12) na Dokar Zaɓe ta 2022 ya buƙaci duk wani mai muƙamin siyasa ya ajiye muƙaminsa kafin ya tsaya wata takara a babban zaɓe.

Hakan na nufin za a tilasta wa wasu manyan ƙusoshin gwamnatin ta Buhari su sauka daga muƙamansu kafin babban zaɓe na 2023.

Buhari ya ce wasu daga cikin tanadin dokar za su haɓaka harkokin zaɓe “kamar 3, 9(2), 34, 41, 47, 84(9), (10), (11) da sauransu”.

“Sai dai abin ba haka yake ba… a sashe na 84 (12) wanda ya shatale masu riƙe da muƙaman siyasa game da zaɓensu da kuma jefa musu ƙuri’a a manyan tarukan jam’iyyu idan ba a gudanar da zaɓen ba cikin kwana 30 kafin zaɓe,” in ji shugaban.

Buhari ya shafe kusan kwana 25 kafin ya sanya wa dokar hannu, wadda ‘yan majalisar suka yi wa kwaskwarima sau biyu kafin ya amince da ita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...

Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya Magantu Kan Zargin raba Ramat da Kujerarsa

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas,...