Daga Aminu Dahiru
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya koma gida da wata lambar yabo wadda Kungiyar mamallaka Kafofin yada labarai na Arewacin Najeriya suka baiwa gwamnan Saboda cancantar sa.
A ranar Litinin din da ta gabata a taronta na shekara karo na 7 da aka gudanar Bristol Palace, da ke birnin Kano, kungiyar mamallaka kafafen yada labarai ta Arewa NBMOA ta bayyana Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin ‘Gwamnan da ya fi kowanne gwamnna yawan kafafen yada labarai a jihar da in banda Jihar Lagos.
Da yake mika lambar yabon ga gwamnan, Shugaban kungiyar Alhaji Abdullahi Yelwa, wanda ya yaba da kyawawan halaye na gwamnan, ya ce Gwamna Abdullahi Ganduje ya kulla kyakykyawar alaka tsakanin gwamnatinsa da kafafen yada labarai.
Tun lokacin da ya hau mulki a shekarar 2015, taken Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya bada tabbacin zai samar da yanayi mai kyau da kuma tallafa muku yan Jaridu don su samun ci gaba a aikinsu.”
Gwamnan ya yi imanin cewa “a matsayin Kafafen yada labaran durka ta hudu a mulkin demokaradiyya, yace kafofin suna taka muhimmiyar rawa a cikin dimokuradiyya da ci gaban kasa.”
Ba wannan kadai ba, gwamnan ya kasance daya daga cikin manyan masu fafutukar kare hakkin yan Jaridu a kasar nan, daga lokaci zuwa lokaci gwamnati na horar da ‘yan jarida tare da ba su damammaki daban-daban.
Tun hawan da gwamnati zuwa yau babu wani dan jarida da aka ci zarafinsa ko aka hana shi gudanar da aikinsa yadda ya dace, Wannan wata dama ce da a kano ne kadai ta Samu.
Duk da haka, don nuna da yadda ya damu da kafafen yada labarai, gwamnan ya busawa Kamfanin buga Jarida na Triumph, bayan rufe ta da gwamnatin data gabata ta yi na rufe Kamfanin ba tare da wani dalili ba.
Bugu da kari, gidan talabijin na Abubakar Rimi da gidan rediyon jihar Kano sun shiga sahun Kafafen yada labaran da suke gogayya Saboda Kayan aiki na Zamani da Kuma hawa Sabon tsarin yada labarai da ya dorasa su a kai.
Ya kamata sauran gwamnonin jihohin kasar nan su yi koyi da Gwamna Ganduje don amfanin al’ummar su.
Aminu Dahiru Shi ne Babban Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Kano akan Hoto
Fabrairu 23, 2022