Daga Sayyadi Abubakar Sadeeq
Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa yan Arewacin Najeriya basu da wanda ya kamata su tasa a gaba ya zama shugaban kasa a Shekara 2023 inba Sanata Bola Ahmad Tinubu ba.
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne yayin taron bude Ofishin Kungiyar Kwararrun Matasan Arewacin Najeriya Masu goyon bayan Tinubu Wato Northern Youth Professional for Tinubu a Kan titin Hadeja Road dake Jihar Kano.
Gwamna Ganduje Wanda Managan Daraktan Hukumar Karota Dr Baffa Babba Dan agundi ya wakilta yace a Zaman wajibi Yan Arewa su ramawa yarbawa abun da sukai musu a Shekara ta 2015 da aka zabi Shugaban Kasa Muhd Buhari.
” Bola Ahmad Tinubu shi ne ya tsaya tsayin data har al’ummar yarbawa Suka goya baya ga Shugaban Kasa Muhd Buhari tun daga zaben fidda gwani na Jam’iyyar APC har ya Zama Shugaban Kasar tarayyyar Nigeria”. Inji Ganduje
Gwamnan yace Lokaci yayi da zasu bayyana wa duniya cewa suna tare da Sanata Bola Ahmad Tinubu don ya kai Kasar nan da Tudun muntsira.
2023: Mai Nada Sarki Zai Iya Zama Sarki – inji Tinubu
A Jawabinsa Shugaban Kungiyar Kwararrun Matasan Arewacin Najeriya Masu son Bola Ahmad Tinubu ya Zama Shugaban Kasa ya bayyana cewa suna son tsohon gwamnan Jihar Lagos Bola Ahmad ya zama shugaban kasa ne saboda duk Kasar nan Babu Wanda ya fi shi son ciyar da kasar nan gaba.
Yace Bola Tinubu Dan kishin kasa ne da idan ya Sami Shugabancin Kasar nan zai kawo cigaba Mai ma’ana ta fuskar Magance Matsalolin tsaro da bunkasa tattalin arzikin Nigeria ta Hanyoyi daban-daban.
Abdullahi Tanko Yakasai yace idan akai la’akari da irin aiyukan Raya Kasa da bola Tinubu ya gudanar a lokacin yana Gwamnan Jihar Lagos , Babu shakka zai iya warware Matsalolin Kasar nan Musamman ta fuskar aiyukan Raya Kasa.
” Mun Yan Arewa Bamu da Wanda yafi bola Tinubu Saboda shi ne ya taimaki Matasa ya Samar musu da aiyukan yi, ya sa su cikin harkokin mulki da Siyasa Saboda kaunar da yake yiwa Matasa ba tare da nuna banbaci yare ko addini ba.
Da yake nasa jawabin Sakataren tsare-tsare na Kungiyar ta NYPT Com. Abubakar baba yawale yace ya kamata yan Arewa sun tabbatar da cewa su Yan halak ne su Mai da biki ga Wanda yayi musu abun alkhairi na goyon bayan Shugaban Kasa Buhari har ya zama shugaban kasar Nigeria.
Yace Shugaban Kasa Buhari ya bayyana musu yadda aka kulla alkawari da Sanata Bola Tinubu a Shekara ta 2013 na cewa Idan Buhari ya gama za a baiwa yan kudu damar Shugabantar Nigeria.
” Mu yan halak ne, mun San halacci Kuma zamu saka haccin da Bola Tinubu ya yiwa mana na amfani da duk damar da yake da ita don Samun nasarar Shugaban Kasa Muhd Buhari.