Daga Rukayya Abdullahi Maida
Fitaccen jarumi kuma mawaki Naziru Sarkin Waka ya baiwa Mama Tambaya kyautar Naira miliyan biyu domin ta fara kasuwanci da magance wasu matsalolinta.
Naziru Sarkin Waka ya bayyana hakan ne a Sahihin Shafin na Facebook.
A makon da ya gabata Mama Tambaya wacce tsohuwar jaruma ce a Kano tun ma kafin zuwan Kannywood ta shaida wa sashen Hausa na BBC cewa ta shiga matsalar Muhalli wacce ta sakata Cikin matsananciyar damuwa, Saboda ta Kasa mallakar Muhalli ko Kama haya Saboda abun da take Samu a fim bai taka Kara ya karya ba.
A hirarta ta Dattawar tace Idan tayi aikin fim ba a ba ta kudin da ya wuce Naira dubu biyu dubu uku Zuwa dubu biyar.
Wannan magana tata ta janyo cece-kuce a masana’antar Kannywood inda wasu suka goyi bayan da’awar Tambaya Wasu Kuma Suka suke ta.
A wani bidiyo da Naziru Sarkin Waka ya fitar ya marawa Mama Tambaya baya inda ya tabbatar wa duniya cewa Tambaya ta fadi gaskiya.
A cewar Naziru ba wai Tambaya Kadai ba da yawa daga cikin jaruman Kannywood haka ake yi musu har ma ya suna fitowa a fina-finan kyauta ba tare da an biya su Kobo ba.