Ra’ayi: Duk Wani Dan Najeriya Yana cin Arzikin Gwamna Tambuwal Ne a Yanzu – Comr. Dahiru Mukhtar

Date:

Daga Mukhtar Dahiru

Sanannen matashin dan gwagwarmayar nan wanda yayi suna wajen tofa albarkacin bakin sa kan al’amurran yau da kullum dake faruwa a Najeriya, Comr. Dahiru Mukhtar, ya ce a halin yanzu duk wani dan Najeriya yana cin arzikin gwamna Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ne na jihar Sokoto.

Comr. Dahiru, ya bayyana hakan ne yau Lahadi a Sahihin shafin sa na facebook, inda yace “Duk wanda ya kwana ya tashi a Najeriya daga shekarar 2014 zuwa yau yana cin arzikin jarumtar gwamna Aminu Waziri Tambuwal.

Mukhtar Dahiru yace Tambuwal shi ne ya jagoranci ceto dimokuradiyyar Najeriya a lokacin da Jonathan ya danne ta zai yi mata yankan Kunkurun Bala”

Da yanzu ‘yan Najeriya mun zama bayi babu mai iya hawa Intanet ya bayyana ra’ayin sa”

“Wannan kawai ya ci mu sakawa (Matawallen Daular Usmaniyya) da kujerar shugabancin Najeriya 2023” Inji Comr. Dahiru Mukhtar

A makonni biyu da suka gabata ne dai gwamna Tambuwal na jihar Sokoto, ya bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaben shekarar 2023 mai zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria

Matatar mai ta dangote ta rage farashin man fetur...

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...