Shekaru 50 Ina fim, amma Naira dubu 2 dubu 3 ake bani in nayi fim – Ladin cima

Date:

Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman

 

Shahararriyar yar wasan Hausa nan wacce take fitowa a matsayin uwa ko kaka  a masana’antar Kanywood Ladin Cima Haruna   ta koka game da yadda ake biyanta kudin Aikin da take yi na fitowa a Fina-finan Hausa.

Kadaura24 ta rawaito Ladin Cima ta bayyana koken nata ne Cikin Wata Hira da suka yi da Sashin Hausa na BBC a cikin Shirin su na “Daga Bakin Mai ita” Wanda a Cikin sa suke tattaunawa da Yan wasan Hausa.
Dattijiwar Wacce ta ce ta kwashe sama da Shekaru 50 tana harkar fim, tace taba shiga Matsalar da ko Yanzu ta tuna ta sai tayi kuka wato Matsalar Rashin muhalli.
Banda Allah ya tsare da yanzu ina bakin bata ina kwana sakamakon matsalar da na shi ga, Amma Allah ya rufamin asiri na fadawa Mutane shi ne Allah ya taimakeni na fita daga cikin Matsalar”.inji Ladin cima
Bayan an tambayi Ladin cima ko ya akai bata tara abun da ta ke samu ba don mallakar Muhallin, sai ta kada baki tace ai ba Wani abun Mai yawa ake bani in nayi fim din ba.
” Ban taba yin Fim an bani Naira dubu 50 ko 30 ko ma 20 ba, Naira duba 5 ce ko 3, yauma na je nayi Aiki Naira duba 2 aka bani to me naci me na ajiye a dubu 2 ko 3?.”
Tace akwai ‘ya’ya 7 da ita take kula da su don haka tace bata da ikon adana Wani abun a Dan abun da ake bata .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...