Daga Sayyadi Abubakar
Gwamnatin Jihar Kano ta ce zata kafa wani Kwamiti na masana da zai tattara tarihin sabbin Masarautun da aka dawo da martabarsu, domin alkinta tarihin don Amfanin al’umma.
Kadaura24 ta rawaito Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan yayin da ya ziyarci Fadar Mai Martaba Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya a Juma’ar nan.
Gwamna Ganduje yace Samar da tarihin Masarautun zai sa Sauran al’ummar duniya su san Cewa Masarautun Suna da tarihin da ya kamata a girmama su saboda shi.
Ya bukaci Sarkin na Gaya daya Fara tattara duk abun da ya Sani game da tarihin Masarautar ta Gaya, domin nan gaba kadan za a kafa Kwamitin tare da Kaddamar da shi domin fara aikinsa.
Gwamna Ganduje ya bada tabbacin Gwamnatin Kano zata cigaba da Kai aiyukan Raya Kasa da cigaban al’umma Masarautar ta Gaya domin Cika burin Gwamnatin na Samar da Kananan burane a Jihar Kano.
Gwamna na Kano ya kuma roki al’ummar sabbin Masarautun da su Maida hankali wajen tallafawa yunkurin Gwamnati na bunkasa Masarautun, ta yadda Masu ikirarin zasu rushe Masarautun baza su iyaba ko da sun Sami dama.
A yake nasa Jawabin Mai Martaba Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya ya yabawa Gwamna Ganduje bisa aiyukan Raya Kasa da cigaban al’umma a Masarautar ta Gaya don Kara inganta ta.
Mai Martaba Sarkin ya Kuma ce ita ma Masarautar tana nata kokarin wajen Ganin an Samar da tituna futilun hanya da Sauran abubuwan da zasu Kara bunkasa Masarautar.