Ganduje zai kafa Kwamitin da zai tattara tarihin sabbin Masarautun Kano

Date:

Daga Sayyadi Abubakar

 

Gwamnatin Jihar Kano ta ce zata kafa wani Kwamiti na masana da zai tattara tarihin sabbin Masarautun da aka dawo da martabarsu, domin alkinta tarihin don Amfanin al’umma.

Kadaura24 ta rawaito Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan yayin da ya ziyarci Fadar Mai Martaba Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya a Juma’ar nan.
Gwamna Ganduje yace Samar da tarihin Masarautun zai sa Sauran al’ummar duniya su san Cewa Masarautun Suna da tarihin da ya kamata a girmama su saboda shi.
Ya bukaci Sarkin na Gaya daya Fara tattara duk abun da ya Sani game da tarihin Masarautar ta Gaya, domin nan gaba kadan za a kafa Kwamitin tare da Kaddamar da shi domin fara aikinsa.
Gwamna Ganduje ya bada tabbacin Gwamnatin Kano zata cigaba da Kai aiyukan Raya Kasa da cigaban al’umma Masarautar ta Gaya domin Cika burin Gwamnatin na Samar da Kananan burane a Jihar Kano.
Gwamna na Kano ya kuma roki al’ummar sabbin Masarautun da su Maida hankali wajen tallafawa yunkurin Gwamnati na bunkasa Masarautun, ta yadda Masu ikirarin zasu rushe Masarautun baza su iyaba ko da sun Sami dama.
A yake nasa Jawabin Mai Martaba Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya ya yabawa Gwamna Ganduje bisa aiyukan Raya Kasa da cigaban al’umma a Masarautar ta Gaya don Kara inganta ta.
Mai Martaba Sarkin ya Kuma ce ita ma Masarautar tana nata kokarin wajen Ganin an Samar da tituna futilun hanya da Sauran abubuwan da zasu Kara bunkasa Masarautar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta dakatar da Dadin kowa, Labarina, Jamilun jidda da wasu fina-finai 19

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   A kokarinta na tabbatar da ana...

2027: Hon Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana Matsayarsa kan takarar gwamnan Kano

Daga Zakariya Adam Jigirya   Dan Majalisar tarayya mai wakiltar kananan...

Sarkin Yaƙin Garko, ya ɗauki nauyin dubawa da raba magunguna kyauta ga marasa lafiyar 1400 a Garko

  Sarkin Yaƙin Garko, mai kishin al'umma, kuma ɗan jam'iyyar...

NAHCON ta yi jigilar Maniyatan Nigeria Sama da 24,000 zuwa Saudiyya a kwanaki 10

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Hukumar Kula da aikin hajji ta...