Wani jirgin yaki da helikwafta sun halaka wasu jagororin ‘yan bindiga masu yawa yayin wani hari da suka kai a jihar Neja da ke arewacin Najeriya.
Rahotanni daga yankin na cewa ‘yan bindigan da yaransu sun kai wasu munanan hare-hare kan wasu al’umomi a kananan hukumomin Kontagora da Mariga da na Rijau a jihar.
Baya ga kashe kananan yara, jaridar PRNigeria ta ce barayin dajin sun kuma washe shaguna baya ga kona gidaje masu yawa da kora shanu fiye da dubu daya da suka yi.
Wani babban jami’in soja ya gaya wa jaridar cewa yanayi maras kyau ne ya hana jiragen yakin na Najeriya kai hare-hare kan ‘yan bindigan.
Amma daga baya rundunar sojojin sama ta aika da wani jirgin yaki samfurin Alpha da wani jirgi mai saukar ungulu zuwa yankin domin daukar mataki kan ‘yan bindign, yayin da sojojin kasa kuma suka biyo bayansu.
Wani wanda ya shaida lamarin ya ce an ga ‘yan bindigan sanye da bakaken kaya na gudu domin tserewa hare-haren.
Shaidan ya kuma ce bayan harin da sojojin saman suka kai cikin jiragen yakin biyu, “an hango ‘yan bindigan da suka tsira da ransu suna gudu kuma sun tafi sun bar gawarwakin ‘yan uwansu da shanun da suka sato warwatse a yankin.”
Daya daga cikin ‘yan bangar yankin ya ce, “mun kirga gawarwaki 37 ciki har da na wasu da muke zaton shugabannin ‘yan bindigan ne”.
A Kaduna
A wani labarin ma alaka da wannan, rundunar sojin sama ta Najeriya ta sanar da cewa jiragen yakinta sun halaka wasu ‘yan bindiga masu yawa a cikin jihar Kaduna.
Sai dai jaridar PRNigeria ta ce wani sojan kasa ya rasa ransa bayan da ya sami mummunan rauni daga harin da sojojin saman ke kai wa, wanda ya rutsa da shi.
Wani wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce ‘yan bindigan na kokarin tserewa daga wani samame da dakarun Najeriya suka kai kan sansanoninsu a Labi kan babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.
Ya ce, “Bayan da barayin dajin sun ci karo da sojojin Najeriya a yankin na Labi, sai suka zabi su sauya hanya domin kauce wa arangamar da ke jiransu.”
Mutumin ya kuma ce bayanan sirri sun taimaka wajen bankado hanyar da barayin dajin ke bi, matakin da ya sa aka tura karin wasu sojojin kasa domin dakile yunkurinsu na tsira.