Daga Zara Jamil Isa
Babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin mai shari’a Maryam Sabo a ranar Alhamis din nan ta yankewa wata mata mai suna Sadiya Ahmadu ‘yar shekaru 27 hukuncin daurin shekaru tara a gidan yari da Kuma aiki wuya, bisa laifin yin garkuwa da wata yarinya ‘yar shekara 3.
A cewar takardar tuhumar da lauyan masu shigar da kara na ma’aikatar shari’a ta jihar Kano, an gurfanar da Sadiya bisa tuhuma daya ta satar mutane.
” Sadiya Adamu ta Titin Badaru, Gayawa, Qtrs, Kano a ranar 22 ga Maris, 2018 da misalin karfe 1100 a Gayawa Qtrs ta yi garkuwa da wata yarinya Khadija Nura, ‘yar shekara 3 da haihuwa da take hannun iyayenta.
Mai gabatar da kara ya sanar da kotu cewa wadda ake kara ta bukaci kudin fansa N1m daga mahaifin Khadija.
Domin tabbatar da Shaida, Lauyan masu gabatar da kara, ya kira iyaye ga wanda abin ya shafa wadanda suka ba da shaida yadda wanda ake kara ta yi garkuwa da ‘yarsu.
Justice Watch News ta tuna cewa tun da farko a lokacin shari’ar, shaidun masu gabatar da kara sun bayyana yadda Sadiya ta yi garkuwa da Khadija daga Gayawa Qtrs da ke karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, aka kai ta kauyen Karaduwa da ke karamar hukumar Matazu ta Jihar Katsina.
Lauyan Mai bada kariya Barista YS Gama ya gabatar da Sadiya wadda ta kare kanta.
A hukuncin da ta yanke, Mai shari’a Maryam Sabo ta tabbatar da cewa Lauyan masu shigar da kara, Barista M.M Farokh ya gabatar da gamsassun hujjoji Waɗanda Suka tabbatar Sadiya ta yi garkuwa da yarinyar.
Mai Shari’ar ta yankewa sadiya hukuncin daurin shekaru 9 a gidan yari tare da yin aiki Mai wahala.
Mai shari’a Maryam Sabo ta kuma umurci mai laifin da ta biya tarar Naira 200,000 ko kuma ta yi shekara daya a gidan gyaran hali.
Ta kuma ba da umarnin a fara yanke hukuncin daga ranar da aka kama ta da kuma tsare ta a gidan gyaran hali.