APC ta kaddamar da Shugabannin jam’iyyar na jahohi 34, banda na jihohi 2

Date:

Daga Halima M Abubakar
 Gabanin babban taron jam’iyyar APC na kasa a ranar 26 ga watan Fabrairun 2022, kwamitin riko na jam’iyyar APC ya kaddamar da shugabannin jam’iyyar na jihohi 34 da kuma babban birnin tarayya.
 Sai dai jihohin Kano da Sokoto ba a kaddamar da shugabannin jam’iyyarsu ba a wani taron da ya gudana a Abuja ranar Alhamis.
 Shawarar kin kaddamar da Shugabannin jihohin na Kano da Sokoto ba zai rasa nasa da rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar a jihohin.
 Jerin sunayen shugabannin jihohin da aka kaddamar a ranar Alhamis kamar yadda PlatinumPost ta rawaito ba sun hadar da;  Dr. Kingsley Ononogbu (Abia), Alh Ibrahim Bilal (Adamawa), Mr Augustine Enefiok Ekanem (Akwa Ibom), Hon Basil Ejike (Anambra), Alh Babayo Aliyu Misau (Bauchi), Dr. Dennis Otiotio (Bayelsa), Mr Augustine Agada  (Benue), Hon.  Ali Bukar Dalori (Borno), da Mr. Alphonsus Orgar Eba Esq.  (Cross River).
 Sauran sun hada da Dattijo Omeni Sabotie (Delta), Hon.  Stanley Okoro Emegha (Ebonyi), Col David Imuse (Edo) mai ritaya, Barr.  Omotosho Paul Ayodele (Ekiti), Chief Ogochukwu Agballah (Enugu), Mr Nitte K Amangal (Gombe), Dr Macdonald Ebere (Imo), Hon.  Aminu Sani Gumel (Jigawa), Air Cdre Emmanuel Jekada (Rtd) (Kaduna), Alh.  Muhammad Sani (Katsina), Alh.  Abubakar Muhammed Kana (Kebbi) da Hon.  Abdullahi Bello (Kogi).
 Sauran su ne Prince Sunday Adeniran Fagbemi (Kwara), Hon.  Cornelius Ojelabi (Lagos), Mr John D Mamman (Nasarawa), Hon.  Haliru Zakari Jikantoro (Niger), Chief Yemi Sanusi (Ogun), Engr Ade Adetimehin (Ondo), Prince Adegboyega Famodun (Osun), Hon Isaac Omodewu (Oyo), Hon Rufus Bature (Plateau), Chief Emeka Turanci (Rivers).  Hon Ibrahim Tukur El-Sudi (Taraba), Alh Muhammed A. Gadaka (Yobe), Alh.  Tukur Umar Danfulani (Zamfara) da Alh.  Abdulmalik Usman (FCT).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...