Zaharadeen saleh
Mai masaukin baki kasar kamaru ta samu nasarar kaiwa ga zagayen wasa na kusa dana karshe a gasar cin kofin kwallon kafa ta kasashen nahiyar Afrika karo na 33 wadda ake gudanarwa yanzu a kasar kamaru.
KADAURA24 ta rawaito Kasar kamaru takai ga zagayen wasan na kusa dana karshen ne bayan data samu nasarar doke kasar Gambia da ci biyu da nema a zagayen wasa na daf dana kusa dana karshe da suka fafata a ranar asabar din nan.
Dan wasan kasar ta kamaru mai suna Toko Ekambi ya samu nasarar jefa kwallo guda biyu araga a mintina 50 da kuma 57.

Haka zalika itama kasar Burkina Faso ta samu nasarar doke kasar Tunisia daci daya da nema ta hannu dan wasanta mai suna Ouattara daya jefa kwallo daya tilo araga ana daf da tafiya hutun rabin lokaci.
A yammacin ranar Lahadin nan ce za’a fafata ragowa wasanin guda biyu na zagayen wasa na daf dana kusa dana karshe a tsakanin kasar Masar da kasar Morocco da misalin karfe biyar na yamma, sai kuma kasar Senegal zata kara wasa da kasar E/ Guinea da misalin karfe takwas na dare agogon Nigeria.