Daga Zubaida Abubakar Ahmad
Kungiyar Tsofaffi Daliban Kwalejin Kimiyya da fasaha ta Jihar Kano bangaren Waɗanda suka karanci Ilimin Gudanar Wato ( school of management studies alumni) ta Karrama Ambassador Yunusa Yusuf Hamza (Falakin Shinkafi) da Lambar yabon mafi girma.
KADAURA24 ta rawaito an Gudanar da taron Karramawar ne a Ranar asabar din nan.
Shugabannin Kungiyar sun ce sun Karrama Falakin Shinkafi ne Sakamakon irin Gudunmawar da ya ke baiwa Ɗalibai don tallafa musu.
“Ambassador Yunusa ya kasance a Koda yaushe baya gajiyawa wajen taimakawa dalibai domin su Sami damar samun Ilimi nagartacce ,ko Kuma taimakawa makarantu”.
“Mun baiwa Falakin Shinkafi Lambar yabo ne ta Mai tallafawa don cigaban Ilimi”.
Da yake Jawabi a wajen taron Ambassador Yunusa Yusuf Hamza (Falakin Shinkafi) ya godewa’ya’yan Kungiyar bisa Karramawar da sukai Masa Cikin dubban Mutanen da suke Kasar nan.
“Wannan Lambar yabon Babu shakka zata karamin kwarin gwiwar cigaba da bada Gudunmawa don cigaban Ilimi”. Falaki
Yace ya Zama wajibi a tallafawa al’umma Musamman Matasa don su Sami ingantaccen Ilimi na addini da na boko, don cigaba al’umma.
“Ina Kira ga mawadata da Shugabanni a kowanne mataki da su Rika tallafawa Matasa don su Sami Ilimi Mai inganci Wanda za a yi alfahari da su a nan gaba, kamar yadda kullum ake cewa Yara Manyan gobe”. Inji Falakin Shinkafi
Taron dai ya Sami halartar Al’umma da dama daga Ciki da wajen jihar Kano.