Daga Muzammil sani yola
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya janye haramcin da ya saka wa Twitter a ƙasar.
Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya tabbatar wa BBC da hakan.
Ana sa ran daga 13 ga watan Janairun 2022 matakin na gwamnatin ƙasar zai soma aiki.
Tun a watan Yunin 2021 ne gwamnatin Najeriya ta haramta amfani da Twitter a ƙasar bayan ta yi zargin cewa ana amfani da shafin wajen kokarin tarwatsa kasar ta hanyar yada labaran karya da ke iya haddasa ”tashe-tashen hankula”.
Hakan ya haifar da martani mai zafi daga ‘yan Najeriya da dama da suke kallon matakin a matsayin taka hakkin bila dama, amma kuma gwamnati ba ta nuna wata damuwa ba, inda ta bar shafin na Twitter a kasar ya ci gaba da kasancewa a toshe.
If you wish for to increase your know-how simply keep visiting this web site and be updated with the most up-to-date
gossip posted here.