Daga Abdulrasheed B Imam
Shugaban Kasa Muhd Buhari ya yabawa Gwamnatin Jihar Kano bisa Shirya taron yiwa Kasa addu’a tare da rokon Gwamnatin data Rika Shirya makamancin taron duk Shekara.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin taron yiwa Kasa addu’a wadanda Gwamnatin Jihar Kano ta Shirya da nufin Samun saukin Matsalolin tsaro da ake fuskanta a Wasu jihohin Kasar nan.
Shugaban Kasar Wanda ya Sami wakilcin Minista a Ma’aikatar aiyukan gona Alhaji Mustapha Baba Shahuri yace an Shirya taron a dai-dai Lokacin daya dace, Inda yace dama addu’a ce kadai hanyar Maganin Matsalolin kasar nan.
Shubaga Buhari ya ce Gwamnatin Tarayya tana iya Bakin kokarin ta wajen wadata Jami’an tsaron Kasar nan da kayan Aikin domin Magance Matsalolin tsaron da ake fuskanta a wasu jihohin Kasar.
A Jawabinsa Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje yace an Shirya taron ne don kaskantar da Kai ga Allah tare da rikonsa ya kawowa Nigeria Saukin Matsalolin da ake fuskanta.
Ya Kuma bada tabbacin duk Shekara Gwamnatin zata Rika Shirya taron Kamar yadda Shugaban Kasa ya bukata, tRe Kuma da yin roko ga Sheikh Dahiru Usman Bauchi da ya Amince da bukatar gwamnatin Kano na gudanar da Mauludin Shehu Ibrahim Inyas na kasa a Kano.
Gwamna Ganduje ya godewa duk mahalatta taron Musamman Khalifan Tijjaniya na Duniya Sheikh Sidi Ali Bil Arabi da Yan tawagar sa bisa halartar Kano da sukai don yiwa Nigeria addu’o’in Samun Zaman Lafiya.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana lokacin taron Addu,a da gwamnatin Kano ta shirya a filin wasa na Sani Abacha da ke nan kano.
Da yake nasa Jawabin Sheikh Dahiru Usman Bauchi Bayan ya yabawa gwamna Ganduje,ya Kuma bada tabbacin za su kawo Mauludin Sheikh Ibrahim Inyas na wannan shekarar Kano Kamar yadda Gwamnan ya roka.
Sheikh Dahiru Bauchi ya Kuma yabawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda ya ke kokari wajen inganta tsaro a kasar nan.
Taron Addu,ar ya samu halartar tawagar gwamnatin Tarayya da wakilan Gwamnonin Wannan Shiyya da Malamai daga bangarori daban-daban da sarakuna da dai Sauran al’umma.