Daga Aisha Abubakar Mai Agogo
Shugabar Kungiyar “Sudu baba fulfulde” Kungiyar dake wayar da Kan Mata Kan harkokin Zaman Aure Hajiya Rukayya Gadon Kaya ta bukaci Mata Musamman Matan Aure su Rika daukar Mazajen su da muhimmanci yadda ya dace .
Kadaura24 ta rawaito Hajiya Rukayya Gadon Kaya ta bayyana hakan ne yayin wani taron wayar da Kan Mata, Wanda ya gudana a garin Dutse babban birnin jihar Jigawa.
Hajiya Rukayya Wacce ta ke ‘yar Jarida ce dake aiki a Gidan Radio Express dake Jihar kano, ta ce ya zama wajibi Mata su rika kula da hakkokin mazajesu Kamar yadda addinin Musulci.
“Ni nayi Imani da duk duniya mijina shi ne maganin dukkan damuwata, Ina Kiran mata da suyi Imani da hakan Kuma Ina kira gare su, su rika girmama mazajensu Dan Allah ya shiga lamarinsu”. Inji Rukayya
Ta ce Allah ne ya ce mata su bi mazajesu Kuma tunda Allah ya fada babu shakka akwai Sakamakon da Allah zai baiwa duk wacce tabi mijinta, Wacce Kuma taki babu shakka zata sha azabar Allah.
Shugabar Kungiyar ta sudu baba fulfulde tace mace wayayyiya ita ce wacce ta ke bin mijinta sau da kafa Kuma ta ke yin duk Wani abun da zai faranta Masa ta ke Kuma barin duk abun da baya so.
“Karya ne dai da ake cewa Namiji ba dan goyo bane, haka ban yarda da cewa duk wacce ta dau Namiji uba zata mutu Marainiya ba, waɗannan karin magana ne da akayi su tun lokacin jahiliya ba na duniyar ilimi ba” Rukayya ta jaddada
Taron dai ya Sami halartar Mata Masu tarin yawa , Waɗanda ake fatan taron wayar da Kan Masu Zai taimaka wajen dinke barakar da take tsakanin Masu fama da rikici tsakanin su day mazajen su , Waɗanda ko suke zaune lafiya da mazajensu zata Kara zaunar da su Lafiya.
Hi, i think that i saw you visited my weblog so i came to “return the favor”.I’m trying to find things to improve my
website!I suppose its ok to use some of your ideas!!