Allah Ya yi wa babban malamin addinin nan na Kano Sheikh Ahmad Bamba Kala Haddasana ya rasu a yau Juma’a.
Wata jikarsa ta tabbatar wa da BBC Hausa labarin rasuwar.
Fitaccen malamin ya yi fice ne a wajen karatuttukan Hadisi, inda a da can yake karantarwar a Masallacin BUK amma daga baya ya bude nasa wajen mai suna Darul Hadis.
Malamin ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya, kuma ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.
Iyalan sun sanar da cewa za a yi jana’izar malamin a Masallacin Darul Hadis da ke unguwar Tudun Yola a birnin Kano bayan Sallar Juma’a.
Za mu ci gaba da kawo muku karin bayani kan labarin.
Allah ya jikan mallam da gafara,