Kungiyoyin Farar hula a Kano Sun bukaci Ganduje ya Sanya Sunan Bashir Tofa a Jami’ar Fasaha ta Wudil

Date:

Daga Safwan Suraj Ilyas

 

Gamayyar Kungiyoyin Farar hula dake Jihar Kano sun bukaci Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya Karrama Marigayi Bashir Othman Tofa ta hanyar sauya Sunan Jami’ar Kimiyya da Fasaha dake Wudil Zuwa Sunan Bashir Othman Tofa.

 

Kadaura24 ta rawaito hakan na kunshe ne Cikin Wata sanarwa da Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Kwamaret Ibrahim A wayya ya Sanyawa hannu Kuma aka rabawa Manema labarai a Kano.

 

Sanarwa tace Bashir Othman Tofa ya chanchanci Gwamnatin Jihar Kano tayi masa wannan Karramawar Idan akai la’akari da irin gudunmawar da ya bayar ta fuskar Siyasar Kasuwanci Ilimi da dai Sauransu a Jihar Kano da Kasa baki daya.

A Cikin Sakon su na ta’aziyya ga Iyalai da al’ummar Jihar Kano Gamayyar Kungiyoyin sun yi fatan Gwamnan Dr Abdullahi Umar Ganduje zai yi duba don karrama gwarzo dan kishin kasa Wanda kano bazata taba mantawa da gudummawar da ba.

 

Sun yi fatan Allah ya gafarta masa yasa aljanna ta zamo makomarsa, ya Kuma baiwa iyalansa da Al’ummar Jihar Kano Hakurin juri Wannan gagarumin Rashi da zai yi wuya a samu Wanda Zai cike gibin da ya Bari.

 

Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito Alhaji Bashir Othman Tofa ya rasu Ranar litinin din data gabata Yana da Shekaru 74 Bayan gajeriyar Rashin lafiya da yayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gidauniyar Pyramid of Heart sun kai tallafin na’urar Oxygen Concentrated Asibitin Murtala dake Kano

Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhd dake Kano ya yabawa...

Da dumi-dumi: ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta fara

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta dakatar da...

Ba mu da wata matsala da Ofishin mataimakin shugaban Kasa – NAHCON

Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta karyata wani rahoto...

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nemi hukumar NBC ta fadada aikinta kan kafafen yada labarai na intanet

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci Hukumar...