Dakarun rundunar Operation Safe Haven ta kama mutum takwas da ake zargi da hannu a garkuwa da wani barasaraken gargajiya a jihar Filato, Charles Mato Dakat.
Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito cewa an saki basaraken a safiyar Juma’a wanda wasu ƴan bindiga suka yi garkuwa da shi a fadarsa da ke Ƙaramar Hukumar Gindiri ta Jihar Filato a ranar Lahadi.
BBC Hausa ta rawaito Mai magana da yawun rundunar ya bayyana cewa sun baza jami’ansu ne inda suka samu nasarar cafke mutanen.
Ana ci gaba da gudanar da binciken mutum takwas ɗin da aka kama waɗanda ake zarginsu da hannu a lamarin.