Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta yi gargaɗin cewa zaɓukan ƙasar na 2023 na iya kasancewa cikin hadari, matukar ba a yi kokarin daƙile matsalar rashin tsaro ba.
A cewar hukumar kalubalen tsaron da ke kara ta’azzara da rashin hukunta masu kawowa shirinta tsaiko ba zai taimaka wajen cimma burinta na yin ingantaccen zabe ba.
BBC Hausa ta rawaito INEC ta ce tun yanzu ta fara tsoron tura ma’aikatan wucin gadi zuwa yankunan da ake fama da rikici, wadanda kuma dole ne a yi zaɓen a cikinsu.
Ta kara da cewa su kansu da yawa daga cikin sama da ma’aikata miliyan daya da ba na dindindin ba da take amfani da su sun nuna fargaba tun yanzu.