Rahoton Binciken Yadda Shanu ke Jigata Idan an Dauke su Daga Arewa zuwa Kudancin Nigeria

Date:

Daga Sani Abdullahi Danbala Gwarzo

 

Babbobi Musamman Dangin su shanu na fuskantar kalubale ya yin da aka debesu daga jihohin Arewa zuwa kasuwannin kudu Musamman jahar lagas.

Dabbobin na fuskantar Kalubalen ne sakamakon irin yadda suke shan wahala kafin su isa daga arewa zuwa kudu, a mafi yawan lokaci dai akan kai dabbobin ne a tsaye wanda hakan yake sawa wasu ke kasa tashi idan sun zauna wasu kuma ke haduwa da karaya ko gocewar Kashi a takaice dai Suna jigata.
 Wakilin Kadaura24 ya da ya ziyarci wasu kasuwannin shanu a jahar lagas, ya sami jin ta bakin wani matashi mai suna Naziru Ya’u dake tsaka da tashin wata shaniya, inda ya bayyana dalilan dake sabbaba irin jigatar da dabbobin suke yi jkafin zuwan su kudu daga arewa.
Yace Suna jigata ne sakamakon dauri da tsayiwa ga kuma tafiya mai nisa wanda  motar shanun takan iya wuce kwana biyu kafin su karasa Jihar ta Lagos Saboda yanayin Motocin da suke daukar dabbobin.
 “Idan mun sami dabbobin da suka jigata sai dai a dauki kurar shanu a dauko su daga mashigar kwata zuwa mayan domin su dabbobin baza su iya takawa da kafafuwansu ba.” Inji Naziru Ya’u
Matashin yace a wasu lokutan ma akan Sami saniyar da ba zata iya ko da yin fitsari ba Saboda da jigata, Inda yace idan suka Sami Waɗanda Suka galabaita to lashakka sai dai kawai a yanka ta.
Irin Wannan nan Matsaloli da dabbobin suke fuskanta babu shakka zasu iya yiwa naman su lahani, Wanda kuma hakan zai iya saukowa har Mutanen da Suka ci naman.
Akwai bukatar dai bukatar masu gudanar da irin wannan sana’ar, su Rika daukar kwararan matakai Waɗanda zasu rika saukakawa dabbobin su rinka isa kudun Cikin hayyacinsu,watakil ko al’umma sa Sami nama mai kyau wanda zai inganta lafiyar su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria

Matatar mai ta dangote ta rage farashin man fetur...

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...